(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

‘Yan Matan Arewa sun bukaci a fara yiwa mazaje gwajin hauka kafin a daure musu aure

Karatun minti 1

‘Yan Matan sun bukaci a fara yiwa maza gwajin hauka kafin aure saboda karuwar duka da maza sukeyi.

A cigaba da shirin Daga Shafukan Instagram, yau ma DABO FM tayi tattaki zuwa shafin nan da mata da mazan Arewa suke tattaunawa matsalolinsu tsakanin samari da ma’aurata.

Wannan mako, matan sun raja’a akan bukatuwar tilastawa mazaje masu neman aure yin gwajin ciwon hauka a lokacin da suke neman aure.

DABO FM ta binciko matan suna cewa; “An fara kaimu makura.”

“Masu matsalar kwakwalwa yanzu sun dena bin bola, babbar riga suke sakawa kuma suyi hada-hada irinta mutane masu hankali.”

“Yakamata a rinka dubawa, shin zai iya rike mata?

Matan sun bayyanawa cewa sun koka kan yadda ‘yan uwa da kawayensu suke basu labarai kan matsalolin da suke fuskanta a zamantakewar gidajensu.

“In bahaka ba, tayaya zamu iya gane mugunta akeyi ko halin rashin ko in kula a cikin gidajen mu.”

Wasu ma daga cikinsu, sun bukaci har ma wadanda suke da auren yakamata a rinka kaisu zuwa duban likitan tabin kwakwalwa kowanne mako.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog