/

An samu sabon ‘Dan Autan’ mawakan hip hop na Hausa bayan rasuwar ‘Lil Ameer’

dakikun karantawa
(H) Marigayi Amir Hassan - (D) Abdullahi Mansur (JBOSS)

Fitaccen mawakin Hausa Hip-hop, Amir Hassan dan asalin jihar Kano da ake yi wa lakabi da dan autan mawakan arewa da Allah ya yi wa rasuwa a shekarar 2017 ya samu magaji.

A lokacin da yaron mawakin ya rasu yana da shekara 14 a duniya, ya kuma rasu sakamakon hatsarin mota.

Sai dai bayan shekaru 3, an sake samun wani sabon yaron mawaki mai suna Abdullahi Mansur da ake yi wa lakabi da Oga_Abdul, dan asalin jihar Jigawa.

Sashin Matasa na DABO FM ta bincika cewar tini dai fitaccen jarumin Hausa, Adam A. Zango ya ayyana daukar matashin zuwa kamfaninshi na White House Family.

A zantawar DABO FM ta matashin, ya bayyana mana cewar yana karatu a Jami’ar Kimiyya da fasaha ta jihar Kano inda a yanzu haka shekara ta 3.

“Suna na Abdullahi Mansur wanda aka fi sani da Oga Abdul, ni haifaffen garin Gujungu ne daga jihar Jigawa. Na yi Firamare a Model Boarding Primary School RIngim, na yi Sakandire a GSTC Karkarna.”

“Yanzu haka ina KUST WUDIL shekara ta 3, ina karantar Biology. Shekarata 19 a duniya.”

Daga cikin wakokinshi akwai Mallam Bahaushe wadda zaku iya kalla a kasa.

 

View this post on Instagram

 

A post shared by j_boss (@iam_oga_abdul) on

Lil Ameer, wanda ake yi wa lakabi da dan autan mawakan hip hop na Hausa ya rasu.

Mawakin, wanda ya yi fice a jihar Kano da wasu yankunan arewacin Najeriya, ya rasu ne sakamakon hatsarin mota yana da shekara 14 a duniya.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog