Labarai

Aisha Buhari tace a rika kiranta da ‘First Lady’ ba uwargidan shugaban kasa ba

Haj Aisha Muhammadu Buhari, ta bada sanarwar chanza sunan matsayinta daga mai dakin shugaban shugaban kasa zuwa ‘First Lady’ ta kasar Najeriya.

Aisha Buhari ta bada sanarwar ne a waje liyafar girmamawa da aka shiryawa matan tsofaffin gwamnonin Najeriya a fadar gwamnatin dake Abuja.

Bisi Olumide Ajayi, daya daga cikin masu magana da yawunta ne ya bayyana sanarwar chanzawar sunan nata.

Sanarwar tace daga yanzu, Za’a rika kiran Aisha Buhari da “First Lady” na jamhuriyar Najeriya.

Wannan ne karo na farko da za’a fara kiran Aisha Buhari da matsayin tin bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu matsayin ‘First Lady’ a kundij tsarin mulkin Najeriya.

Inda ya bayyana cewa bazai bawa matarshi ofishin ‘First Lady’ domin batada wani aiki a dokance.

Dabo FM ta rawaito cewa; Shugaba Muhammadu Buhari yakance, maganar matata, magana ce kamar ta kowanne dan Najeriya da yake da yan fadar albarkacin bakinshi.

Tanayin magana ne bada yawun gwamnati ba.

Karin Labarai

Masu Alaka

Iyalan Buhari na da damar daukar jirgin shugaban kasa suyi harkokin gaban su -Garba Shehu

Muhammad Isma’il Makama

Hannunka Mai Sanda: Aisha Buhari ta kara caccakar shugaba Buhari

Dabo Online

Aisha Buhari ta yiwa Mamman Daura da Garba Shehu kaca-kaca a Villa

Muhammad Isma’il Makama

Hanan Buhari ta kammala digiri da maki mafi daraja

Muhammad Isma’il Makama

Aisha Buhari ce ta assasa cire mukamin da Sanata Ahmad Lawan ya bayar

Dabo Online

Aisha Buhari ta halarci taro da rigar naira miliyan 1.6

Dabo Online
UA-131299779-2