Kungiyar yan jaridu ta Kasa shiyyar Zariya a Jihar Kaduna, ta sake nanata kudirin ta na aiki kafada da kafada da sauran kungiyoyi domin sammar da cikakken ‘yancin ga kowanne dan kasa domin ribatar damar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya shi na yin mu’amalar sa ba tare da tsangwama ko cikas ba.
Shugaban Kungiyar Muhammad Bello Habib ya bayyana hakan sa’ilin da ya karbi bakuncin wata Kungiyar da ke rajin kare hakkin al’umma da taimakon matasa domin inganta rayuwar su mai suna Human Right and youths empowerment a turance.
Ya ce, abun takaici ne yadda a kasar nan masu karamin karfi ke samun cikas duk lokacin da suka fuskanci wata kalubalen rayuwa, wanda sukan rasa masu tallafa masu domin kaiwa ga nasarar yakar abun da ya hana su sakat.
Inda ya koka kan matsalar rashin yawaitar kungiyoyin kare hakkin dan adam da za su rika zama jagora a wasu lamuran.
Muhammad Habib, ya yaba ma Kungiyar ta Human Right and youths empowerment saboda yadda suke gudanar da ayyukan su na bibiyan bahasin wasu da aka zalunta, ya kuma hori membobin su jajirce da gwagwarmayar da suka faro domin kaiwa ga tudun mun tsira.
Da yake nashi jawabin shugaban Kungiyar Malam Abdullahi Muhammad ya ce, sun zo ziyarar ne da nufin kara yaukaka dankon zumunci da Kungiyar ta NUJ shiyyar Zariya, wanda ta kumshi kananan hukumomin shiyya ta daya a Jihar Kaduna. kasancewar su ma suna gudanar da ayyukan su a Kasa baki daya da kuma nan Jihar Kaduna da fatan samun nasarar lalubo hanyoyin magance yawaitar cin zarafin kananan yara da ake ta hanyar yi masu fyade ko muzhuna masu wasu ma takan kai ga kisa a wasu lokutan.
