Labarai

Gwamnatin jihar Kano ta haramta lika hotuna ko rubutu a jikin motoci da babura masu kafa 3

Hukumar dake kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano ‘KAROTA’ ta haramta lika duk wasu nau’ikan hotuna a jikin baburan Adaidaita sahu da motoci a jihar Kano.

GIdan Rediyon Freedom dake jihar Kano ya rawaito cewa hukumar tace wajibi ne dukkanin masu ababen hawa suyi biyayya ga dokar.

A cewar hukumar daukar matakin ya zama wajibi sakamakon cewa hotunan kan dauki hankulan Direbobin masu tuki wanda ke sanadiyyar afkuwar hadari.

DABO FM ta binciko cewa mutanen jihar Kano masu baburan adaidaita sahu da motoci, suna lika hotuna ko nau’in rubuce-rubuce a jiki domin nuna soyayya.

Har ma masu kamfanunuwa sukan baiwa masu baburan ‘yan kudade domin su tallata hajarsu ta hanyar lika hotunan kamfanin a jikin baburin nasu.

Haka zalika, a jihar Kano, lika hotunan yan wasan kwaikwaiyo a jikin adaidaita sahu ko motocin haya ya zama ruwan dare, inda bincike DABO FM ya tabbatar da samun babur ko mota da hotan ‘yar wasan kwaikwaiyo a duk ranar da mutum ya fita titi a jihar ta Kano.

Karin Labarai

Masu Alaka

Akwai yiwuwar hana sana’ar tuka ‘Babur mai kafa 3’ a jihar Kano – Dan Agundi

Dabo Online
UA-131299779-2