(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');
//

Crowwe: Sabuwar manhajar sada zumunta mai dauke da asusun ajiyar kudi kirkirar dan Najeriya

Karatun minti 1

Sabuwar manhajar Crowwe, manhaja ce ta sada zumunta mai fasali da ya kunshi irin na manyan manhajojin sada zumunta irin su Facebook, Twitter da Instagram.

Mai amfani da manhajar zai iya sanya hoto, bidiyo, ya kuma tura sako ga yan uwa da abokan arzuka.

DABO FM ta bincika cewa manhajar tana dauke da asusun ajiyar kudi da zai ba wa mai amfani da ita damar siyen katin waya, biyan kudi ga wasu kamfanoni da ke karbar kudi ta yanar gizo musamman masu samar da Intanet.

Duk da ana alakanta masu kamfanin manhajar da siyasa, wani daga cikin masu ruwa da tsaki a kamfanin da ke lura da manhajar ya tabbatar da cewa “babu abin da ya hada manhajar da siyasa ko wani dan siyasa.”

Kamar kowacce manhaja, ana bukatar mai son amfani da ita ya sanya Email, sunan da ake so ayi amfani da shi, hoto da kuma lambobin sirri da za su kare masu kutse da shiga shafin mai amfani da ita.

Ma su wayoyin Andriod da Apple za su iya samun manhajar a rumbun ajiyar manhajoji na Google Play Store da kuma Apple Store kai tsaye ba tare da biyan ko sisi ba.

Manhajar kyauta ce, ba ta bukatar mai amfani da ita ya saka kudi ko ya biya kudi domin yin amfani da ita.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog