/

Kwana 355 da ɗaukewar ‘babu gaira babu dalili’ da aka yi wa Abu Hanifa Dadiyata

Karatun minti 1
Abubakar Idris Dadiyata

Matashi Abubakar Idris Dadiyata ya cika kwanaki 355 tin bayan da wasu da ba a san ko su waye ba su ka ɗauke matashin har gida.

Zuwa yanzu, dangin matashin sun kai ƙarar Gwamnatin jihar Kaduna, hukumar DSS reshen jihar Kaduna zuwa gaban kotu su na tuhumarsu a kan batan matashin.

Tin a ranar 1 ga watan Agustar 2019, rahotannin sun bayyana yadda wasu mutane da ba a san ko su waye ba, suka je har gidan matashin da ke jihar Kaduna, su ka ɗ aukeshi, lamarin da ya yi sanadiyyar har zuwa yanzu babu labarinsa.

Hukumar DSS da aka zarga tin a farko, ta bayyana cewa ba ta da hannu, hasalima ba ta tura jami’anta unguwar da matashin yake ba, a ranar da ake zargin an ɗaukeshi.

Dadiyata, malami ne a jami’ar Katsina, ya kasance ɗan gwagwarmaya da fafutukar ganin gwamnatin APC a Najeriya da jihar Kano sun yi adalci a jagorancinsu.

Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Abu Hanifa Dadiyata, ɗan Jami’iyyar PDP ne, mabiyin kungiyar Kwankwasiyya waɗanda su ne manyan abokan hamayyar gwamnatin jihar Kano da Dr Abdullahi Ganduje ya ke jagoranta.

Manyan mutane a Najeriya sun yi Allah-Wadai da rashin matashin, kazalika, hukumomin kare hakkin dan Adam na duniya sun biye musu sahu wajen kiran waɗanda su ke tsare da shi da su sake shi.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog