Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa, EFCC ta chafke tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani.
Kamar yadda majiyar mu ta Dabo FM ta bayyana mana, EFCC ta kame shine bisa zargin laifin cin amanar kasa, tare da karbe wa shugaban kamfanin saida motoci na ASD Motirs zunzurutun kudi har $20,000.
TheNation ta bayyana cewa “An kama shi ne bisa zargin karbar dalar Amurka har Dubu Ashirin, kimanin Naira Miliyan 7.2 da cewar shi makusanci ne ga Shugaban Hukumar ta EFCC, Ibrahim Magu.”
“An tabbatar da kama shi sannan an sake shi a kan beli, bayan da ya biya mai karar kudinsa cif da cif.”
Majiyar ta kara da cewa “Da jimawa mun gayyace shi amma kemadagas yaki zuwa, muna zargin yana cutar mutane da sunan shugaban hukumar ta EFCC.”
Cikakken rahoton na nan tafe…
