//
Friday, April 3

EFCC ta cafke Kwamared Shehu Sani bisa tuhumarshi da damfarar Naira miliyan 7

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar dake hana yi wa tattalin arziki ta’annati ta EFCC, ta damke tsohon Sanatan jihar Kaduna, Kwamared Shehu Sani bisa zarginshi da damfarar Naira miliyan 7.

Jaridar The Nation, ta rawaito cewa wata majiya ta bayyana mata zargin da hukumar EFCC take yi wa Shehu Sani.

Majiyar tace Sanata ya karbi kudi, dalar Amurka har 20,000 daga mai kamfanin motoci na ASD.

Majiyar tace ya karbi kudin ne a matsayin toshiyar baki da zai bawa shugaban hukumar ta EFCC.

Majiyar ta kara da cewa ya karbi kudin bayan ya nunawa kamfanin yana da kusanshi tsakaninshi da hukumar EFCC

Cikakken bayani yana zuwa….

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020