Zazzabin Lassa, ciwo ne da kan iya jawo mutum ya rika zubar da jini ta kowace mafaka (hanci, baki, ido, da sauransu), har ma Idan abin ya zo da ajali, ya raba mutum da duniyar baki daya. A halin yanzu ana annobar wannan cuta a Najeriya har cutar ta kashe mutum uku a asibitin Malam Aminu Kano.
Cikin wata tattaunawa da wakilin Dabo FM, Dokta Abdul’aziz Tijjani kwararren likita ne a birin Taxes dake kasar Amurka, Dokta yayi bayani dalla dallah yadda ake kamuwa da wannan sabuwar cuta da turawa ke kira da Zazzabin Lassa.
Dr ya bayyana cewa: Wannan cuta ta zazzabin Lassa beraye ne ke yada ta ta hanyar yin fitsari da bahaya akan kayan abinci da abubuwan amfani na yau da kullum kamar kwanuka, farantai da cokula. Idan mutum ya yi amfani, wurin ci ko sha, da wadannan abubuwa da beraye suka gurbata zai iya kamuwa da wannan cuta.
Za kuma a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa ta hanyar shakar iskar da ta gurbata da fitsari ko kashin beraye ko kuma ta hanyar cin berayen da suka kamu da wannan cuta a matsayin abinci.
A wasu lokutan, musamman a asibitoci da wuraren kiwon lafiya, ana iya daukan zazzabin Lassa daga mutanen da suka kamu cutar ta hanyar cudanya da jinni ko ruwan jikinsu. Ma’aikatan asibiti da yan uwan maras lafiyar su suka fi kowa hadarin daukar cutar daga wanda ya kamu.
Bayan sati daya zuwa uku da kamuwa da wannan cuta, kimanin kashi tamanin bisa dari na wadanda suka kamu da cutar zazzabin Lassa za su iya fara nuna masassautan alamomi na kamuwa da cutar. Masassautan alamomin Lassa da suke fara bayyana sun hada da zazzabi, mutuwar jiki da ciwon kai.
Ragowar kashi ashirin bisa dari kuma na iya kamuwa da zazzafar cuta da ka iya bukatar sai an kwantar da su a asibiti. Bincike ya nuna cewa Kimanin kasha sha biyar bisa dari na wadanda aka kwantar a asibiti sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa su ka riski ajalinsu ta hanyar cutar.
Alamomin zazzafar lassa sun hada da: zazzabi, zubar da jini da zai iya faruwa ta kowace kafar jiki kamar baki, hanci, da sauran su; yin lumfashi da kyar; amai (musamman aman jinni), kumburin fuska, ciwon jiki, kurmancewa, da gushewar hankali.
Za mu iya kare kawunan mu daga kamuwa da cutar zazzabin Lassa ta hanyoyi masu sauki kamar haka:
• Mu toshe ramukan beraye a gidajenmu
• Mu kula da kayan abinci mu saka su a wurin da bera ba zai iya samun mu’amala da su ba
• Mu kai maras lafiyan da ake zargin yana da cutar asibiti da gaggawa, a killace wannan maras lafiyar daga sauran marasa lafiyan asibiti
• Ma’aikatan asibiti da iyalan maras lafiya su tabbatar sun saka kayan kariya kafin su yi muamala da maras lafiyar da ake zargin yana da wannan cuta
• Mu guji cin naman beraye
Daga karshe, Hausawa su kan ce riga kafi, ya fi magani.
