/

Kano: Mutane 176 ne suka rasa ransu sakamakon hadarin jirgin sama a rana irin ta yau

Karatun minti 1

Jirgi mai kirar Boeing 707 ya fadi a jihar Kano yayin da yake kokarin sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 176 a cikin shekarar 1973.

Rahoton Dabo FM na ranar tunawa da tarihin babban hatsari mafi girma da ya taba faruwa a fadin Najeriya cikin ranar 22 ga Junairu 1973 a jihar Kano wanda ya halaka kimanin mutane 176, ragowar mutane 26 suka jikkata.

Makamancin wannan hadari ya kara faruwa a jihar Kanon cikin shekarar 2002, wanda shima jirgin sama ya fadi a cikin unguwanni dake cikin garin na Kano, unguwar da hatsarin yafi shafa ita ce Gwammaja, wannan mummunan hadarin yayi sanadiyar mutuwar fiye da mutane 155, daruruwan mutane sun jikkata.

Jirgin EAS Airline mai tagwayen inji kirar British-built BAC 1-11-500 ya baro jihar Lagos zuwa Kano da mutane 76 tare da ma’aikatan jirgin mutum 8 a cikin sa, cikin harda ministan wasanni, Ishaya Mark Aku, fasinjoji 4 da ma’aikacin jirgin 1 ne suka rayu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog