Home LabaraiGanin sabon dan majalisar PDP da ya kayar da Kofa tare da shugaban APC ya jawo cece-kuce

Ganin sabon dan majalisar PDP da ya kayar da Kofa tare da shugaban APC ya jawo cece-kuce

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Hotunan sabon zababben dan majalisar Kiru da Bebeji na jam’iyyar PDP, Ali Datti Yako da shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Abbas a lokacin karbar satifiket ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.

Majiyar Dabo FM ta bayyana dama dai tini ake ta rade-radin jam’iyyar ta APC ‘anty party’ tayi wa tsohon dan majalisar Kiru da Bebejin, Abdulmumin Jibrin Kofa wanda yasha kayi da tazarar kuri’a fiye da dubu 35.

Bayan faduwar zaben nasa Kofa ya bayyana shifa bazai je kotu ba.

Cikin fuskokin wadanda ma’aikatan Dabo FM sukayi ido hudu dasu wajen rantsar da sabon dan majalisar PDP din akwai jiga-jigen kwankwasiyya, kana harda yan majajisun jam’iyyar APC musamman na karamar hukumar Dala, Babangida Alasan Yakudima, da kwamishinoni dama wasu bila adadin.

Dabo FM tayi duk mai yiwuwa domin jin ta bakin Ali Datti Yako akan ko dama can suna da wata yarjejeniya da jam’iyyar APC amma abin yaci tura.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00