Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, namijin jiya, ‘an rasa har yau ana mora’

A watan Afirilun 2020, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, zai cika shekaru 13 tin bayan da wasu da ba’a san ko suwaye ba suka kashe shi yayin da yake sallah a masallacinshi dake jihar Kano.

DABO FM tayi duba tare da nazarin bincike kan yadda wasu daga cikin karatuttukan malamin suke fito wa duk lokacin da aka shiga wani yanayi ko wata matsala ko annoba da ta tunkaro al’ummar musulmin Najeriya.

Akan samu kalaman da malamin yayi akan fadar laifi ko halin wani daga cikin shuwagabanni da jagorori a Najeriya.

Binciken DABO FM ya nuna cewar yakan zama abu mai wuya a samu wata mas’ala da ta yadu wacce karatun da malamin yayi akanta bai fito ba, har ma dayawa akan ce “kamar Mallam yana nan akayi wannan abun” ko “kamar Mallam yasan za’ayi haka.”

Masu Alaƙa  Yi wa Mata kaciya ba Addini bane, muguwar Al’ada ce kuma cutarwa ne -Sheikh Gumi

DABO FM ta tattara wasu daga cikin karatuttukan malamin wadanda yayi magana akan wasu al’amura da a yanzu ake tsaka da tattauna su.

. Farkon farawa da al’amarin hukunci da wata kotun majistire a birnin Abuja ta yanke wa Maryam Sanda na kisa ta hanyar rataya bayan samun ta kashe mijinta, Bilyaminu Bello a shekarar 2017.

Bayan hukunci, dayawa daga cikin al’ummar Musulmin Najeriya sun yi nuni cewa babu wata hanyar kubutar Maryam Sanda har sai an kashe ta kamar yadda shari’ar addinin Musulunci tace.

Anan ne karatun malamin ya zama ruwan dare, inda DABO FM ta tattara malamin yana fadar mafitar da za’a nema wanda shari’ar zata hana a kashe Maryam Sanda.

. A watan da ya shude kafin cikar sabuwar shekara, zancen Jaruma Rahama Sadau akan shigar da tayi a ranar bude sabon wurin gyara jiki da ta bude a jihar Kaduna, ya janyo cece-kuce ganin yadda mutane suka bayyana shigar a matsayin wacce ta saba ka’idar musulunci. A lokacin, an fitar da karatun Marigayi Sheikh Ja’afar da yayi magana akan irin mata da suke saba wata ka’ida ta musulunci wanda aka alakanta da shigar Rahama Sadau.

Ga dai abinda marigayin yace;

Saurara anan.

Akwai magan-ganu da dama akan wadansu jagorori da shuwagabannin daga sashin arewaci da kudancin Najeriya wadanda baza su saka anan ba saboda wasu dalilai.

Masu Alaƙa  Yunwa, Talauci, Tashin hankali da bala'i kawai ake fama dashi a Najeriya - Sheikh Muhd Nasir

Bayan rasuwar 12 da rasuwar Sheikh Ja’afar, a iya cewa har yanzu ana morar irin tagomashin baiwar da Allah ya baiwa marigayin ta hanyar yin bayanin dake gamsar da dukkanin masu sauraronshi da daliban Ilimi.

Sai dai tin bayan kwanta damar malamin har yanzu ba’a samu wanda ya maye gurbinshi ba musamman wajen fadar gaskiya a kan kowanne mahalukin shugaban mulki ko na sarauta.

Ana ganin malamai irinsu Sheikh Ibrahim Makari, limamin babban masallacin Abuja da Sheikh Isa Ali Pantami, ministar sadarwa da kimiyyar zamani, na daga cikin malamai masu karancin shekaru da suke bada karatu cikin fasahar magana da tarin ilimi.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.