Kiwon Lafiya

Barin kumfar man goge baki a baka na inganta lafiyar hakora -Binciken Likitoci

Wani kwarerren likitan hakora dake Jami’ar Maiduguri jihar Barno Lawal Balami shine ya tabbatar da haka inda ya kara da cewa rashin sani na daga ciki matsalolin dake haddasa cututtukan hakora da mafi yawan mutane a Najeriya ke fama da su.

Majiyar Dabo FM ta jaridar PremiumTimes Hausa ta bayyana cewa Dokta Balamia ya kara da cewa ya kamata mutum ya wanke hakorar sa sau biyu a rana sannan a duk wanki a dauki akalla mintuna biyu ana goge hakora.

Sannan kuma barin kumfar man goge baki a cikin baki na inganta aikin sinadarin ‘Fluoride’ da ka yi man da shi.

Ya ce sinadarin fluoride sinadari ne dake karfafa karfin hakorar mutum, hana warin baki sannan da kare hakorar mutum daga kamuwa da cututtuka.

Lawal ya ce idan za a iya a daina kuskure baki bayan a kammala gogewa, mai makon haka a yi amfani da ruwan ‘Mouth wash’ a wanke hakora da shi.

A dalilin haka wani likita a shafinsa na tiwita yayi kira ga mutane da su daina dauraye bakunan su da ruwa bayan sun goge hakoran su da magogi cewa yin haka na kara inganta tsaftar baki.

Wannan ya biyo bayan sakamakon wani bincike da kungiyar kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi ya nuna cewa kashi 15 zuwa 58 na mutane a Najeriya na yawan kamuwa da cututtukan dake kama hakora.

Binciken ya kuma kara nuna cewa kashi 30 bisa 100 daga cikin su kan dade suna fama da wadannan cututtuka ba tare da sun je asibiti ba.

Hakan na da nasaba ne da rashin wanke hakora yadda ya kamata da mutane ke yi.

Bayan haka sakamakon binciken da ‘National Smile Mouth’ ta gudanar ya nuna cewa mutane Biyu cikin mutane Uku a Najeriya basu da masaniya game da yadda ya kamata wanke baki da hakora.

Masu Alaka

Zogale yafi kaza: Najeriya zata shuka zogalen naira Biliyan 9

Muhammad Isma’il Makama

Lemon Tsami yana kare jiki daga daukar cutar “Cancer”, Daga Dr Guru Prasad

Dabo Online

Mata suna gane Namijin dake musu karya ‘Ido na Ganin Ido’ – Masana

Dabo Online

Mata masu tabin hankali a Najeriya sunfi ‘yan kasar Canada, Morocco da Andalus yawa

Dabo Online

Kashi 6 cikin 10 na matan Najeriya, sunada tabin hankali -Masana Kwakwalwa

Dangalan Muhammad Aliyu

Yanzu babu cutar ‘Polio’ a Najeriya – WHO

Dabo Online
UA-131299779-2