Ana saka ran dawowar Sheikh Kabiru Gombe da Bala Lau gobe Talata daga Amurka

Shugaba da Babban sakataren kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sheikh Muhammad Kabir Gombe suna kan hanyarsu ta dawo wa gida Najeriya.

Ana sa ran isowar malaman a gobe Talata, 30 ga watan Afirilun 2018 da Asuba.

Tin dai farkon tsakiyar watan Afirilun ne malaman suka je kasar Amurka domin wakiltar kungiyar Izalatu Bidi’a wa ikamatus Sunnah a wadansu tarurrukan addnin Musulunci a kasar Amurka.

Daga cikin ziyarar bude da malaman biyu sukayi, sun ziyarci dakin taro na majalissar dinkin Duniya “United Nation Assembly.”

Sai dai tafiyar malaman ta janyo cece kuce inda akayi ta yada wasu bidiyoyi da suka nuna Sheikh Kabiru Gombe a cikin karamin jirgin ruwa tare da matarshi.

Ana yada bidiyon ne tare da bayanin cewa sun karbi kudin yakin neman zaben shugaba Buhari ne inda sukaje kasar Amurka domin kashe kudin kamar yadda Sheikh Gombe a wani bidiyo da yayi na musanta bidiyon da ake yadawa, inda yace bidiyon anyi shine lokacin da sukaje kasar Saudiyya a shekarar data wuce.

Gidan Talbijin na Nishadi TV yace ana sa ran isowar malaman a gobe Talata da asubar Najeriya da Nijar.

%d bloggers like this: