Copyrighted.com Registered & Protected

Dalibai suna zanga-zanga a ofishin jakadancin Saudiyya dake Kano kan Zainab Aliyu

A safiyar yau Talata, dalibai a jihar Kano suka shirya zanga-zangar lumana domin kira ga ceto rayuwar Zainab Aliyu.

Zanga zangar tana zuwa ne dai dai lokacin da al’umma Najeriya ke kokawa batun dalibar ‘yar asalin jihar Kano wacce hukumomi a kasar Saudiyya suka tsare bisa zargin shigar da haramtacciyar kwaya kasar.

An fara zanga-zangar ne da misalin karfe 9 na safe, inda aka tsara za’a fara zuwa gidan mai martaba Sarki, Mallam Sunusi II, inda daga nan kuma za’a dan gana zuwa fadar gwamnatin jihar Kano, daga karshe z’anufi ofishin jakadancin kasar Saudiyya dake birnin Kano.

Daga shafin Abba Ibrahim Gwale.

Hotuna:

Bayyana ra'ayi a sahafinmu na Facebook
Masu Alaƙa  Ganduje ya gwangwaje Zainab Aliyu da Naira Miliyan 3 bayan fitowarta daga hannu Saudiyya

Gargadi

Ba'a yarda wani kamfanin Labarai ko shafi yayi amfani da Rahotanninmu ba tare da tuntubarmu ba. Tuntube mu ta "submit@dabofm.com
%d bloggers like this: