A cewar Daily Trust, sunayen mutane 37 da ake zargin masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne, waɗanda suka mutu a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Neja, sun fito.

Mutanen sun kasance cikin waɗanda jami’an NSCDC suka kama a lokacin samamen da suka gudanar a ranakun 15 da 16 ga watan Satumba, a yankin Estate na Laftanar Janar Mohammed Inuwa Wushishi da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

A cewar hukumar a lokacin, an gano cewa wasu daga cikin mutanen da ake tsare da su sun mutu a safiyar ranar 17 ga Satumba, bayan wani abin da hukumar ta bayyana a matsayin zargin barkewar wata cuta. Hukumar ta ce za a gudanar da binciken lafiya domin gano ainihin abin da ya haddasa mutuwar.

Lamarin ya sa gwamnatin tarayya ta dakatar da jami’an da abin ya shafa tare da kafa wani kwamiti mai zaman kansa domin binciken yadda lamarin ya faru, ciki har da yadda aka kama da kuma tsare mutanen da kuma musabbabin mutuwarsu.

Awaisu Giwa, jakadan zaman lafiya na kasa da kasa na International Human Rights Commission (IHRC), ya ce an samo jerin sunayen farko daga bayanan asibitin General Hospital da ke Minna.

Ya ce an ƙara wasu sunaye huɗu bayan wasu ‘yan uwa sun tuntubi hukumar domin sanar da ita cewa ba a saka sunayen ‘yan uwansu a cikin bayanan farko ba. Ya kuma bayyana cewa za a yi amfani da jerin sunayen wajen taimaka wa iyalan waɗanda suka mutu wajen samun diyya.

Sunayen mutanen 37

  1. Ibrahim Sani
  2. Fahad Sa’adu
  3. Abdulsalam Ismail
  4. Usman Aliyu
  5. Abubakar Alhaji
  6. Sani Nasir
  7. Sanusi Khalid
  8. Ahmad Aliyu
  9. Safiyanu Abdullahi
  10. Suleiman Dantala
  11. Idris Haruna
  12. Sani Yakubu
  13. Safiyanu Abubakar
  14. Abdullahi Abubakar
  15. Abubakar Musa
  16. Abdul Mudassir
  17. Suleiman Lawal
  18. Usman Abdullahi
  19. Samuel Sambo
  20. Ibrahim Musa
  21. Yusuf Nasiru
  22. Umar Lawal
  23. Isyaku Amisu
  24. Bissallah Adamu
  25. Abdulbari Suleiman
  26. Shafisu Lado
  27. Usman Ahmad
  28. Usman Ibrahim
  29. Sani Isyaku
  30. Musa Ibrahim
  31. Idris Bashir
  32. Kabiru Suleiman
  33. Emmanuel Emeka
  34. Mu’awiya AbdulKarim
  35. Abdul Gafar Abubakar
  36. Usman Haruna
  37. Yaro Salihu Soba

A cewar bayanan da suka kasance tare da jerin sunayen, Mu’awiya AbdulKarim, Abdul Gafar Abubakar, Usman Haruna da Yaro Salihu Soba ba sa cikin jerin farko na General Hospital, Minna, kuma an ƙara sunayensu ne bayan ‘yan uwansu sun tuntubi hukumar.