Zagin Shuwagabanni da Malaman Addini tamkar zubar da jini ne – Dr Rijiyar Lemo

dakikun karantawa

Sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, yayi kira ga musulmai da su guji zagi da cin mutuncin yan uwansu musulmai da shuwagabanni musamman a kafafen sadarwa.

Malam ya fara da cewa:

“Wannan lamari yana ba ni tsoro…!

Yau an wayi gari mutuncin Mutane ya zama abin banza. Kowa bai wuce a keta masa mutunci a ci zarafinsa a fito a zazzage shi a bainar jama’a ba. Musamman a wadannan kafafe na sada zumunta Facebook, Tweeter, Instagram da makamantansu.

A yau babu wani shugaba da yake da kwarjini da ake jin tsoron zaginsa…
Babu wani Sarki da yake da martabar da za ta sa a kiyaye matsayinsa…
Babu wani Malami da yake da alfarmar da za ta sa a kiyaye darajarsa…
Babu wani shugaban al’umma da yake da matsayin da zai sa a kare masa mutuncinsa…

Haba Jama’a, Mutuncin Musulmi fa kamar Jininsa yake!

Cin mutuncin Musulmi da Zubar da kimarsa dadai yake da zubar da jininsa.

A yau kowa ya fito yana ta kururuwa a kan zubar da jinane da suke faruwa a sassasa daban-daban na Kasarmu, amma a lokacin da yake wannan kururuwa, a lokacin ne yake cin mutunci da zubar da kimar Musulmi.

A bisa hakika, kai da kake cin mutuncin Musulmi a Facebook, dadai kake da wanda yake zubar da jini a Jihar Zamfara.

Annabi (saw) a ranar Hajjin Ban-kwana ya ce:
«فإن دماءكم وأموالكم وأعراضكم عليكم حرام، كحرمة يومكم هذا، في بلدكم هذا، في شهركم هذا»
صحيح البخاري (2/ 176) صحيح مسلم (3/ 1306)

“Lallai jinanenku, da dukiyoyinku, da MUTUNCINKU, HARAMUN NE A KANKU, kamar haramcin wannar ranar taku, a wannan gari naku (Makka), a wannan wata naku”.

Imamu Nawawiy ya ce:
معناه متأكدة التحريم شديدته، وفي هذا دليل لضرب الأمثال وإلحاق النظير بالنظير قياسا
شرح النووي على مسلم (8/ 182)

A wani Hadisin kuma:
«بحسب امرئ من الشر أن يحقر أخاه المسلم، كل المسلم على المسلم حرام، دمه، وماله، وعرضه»
صحيح مسلم (4/ 1986)

“Ya ishi mutum samun sharri ya WULAKANTA DAN UWANSA MUSULMI, kowane Musulmi haramun ne a kansa ya zubar da jinin Musulmi, ko ya ci dukiyarsa, ko ya ci mutuncinsa”.

Malamai suka ce: Mutunci shi ne muhallin yabo ko zargin mutum, sawa’un a kansa ko a danginsa.

Haba Jama’a, wannan fa Musulmi kawai aka ce, ina kuma ga Jagororin Musulmai?
– Shugabannin Gomnati.
– Sarakunan Musulmai.
– Malaman Addini.
– Shugabannin al’umma.

Rashin Tarbiyya ne da rashin riko da Addini ka mayar da dandalin Facebook da ire-irensa ya zama dandalin cin mutuncin Dan uwanka Musulmi, balle kuma shugabanni a cikinsu.

Shin al’ummar nan za ta dore kuwa, idan aka ci mutuncin kowa, aka rasa mutunta shugabanni?!
Yanzu kenan zamu wayi gari babu mai mutuncin fada aji kenan a cikinmu?!”

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog