Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Farfesa Attahiru Jega ya shiga Jami’iyyar PRP

2 min read

Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega, ya shiga jami’iyyar PRP ta Mallam Aminu Kano.

Sakataren yada labaran jami’iyyar, Abdul Gombe ne ya bayyana haka a wata takarda mai dauke da sa hannunshi.

Ya bayyana cewa Farfesa Jega zai shugabanci kwamitin fadi-tashi na jami’iyyar wanda zai yi duba game wajen mayar da jami’iyyar yin karfi a kasa baki daya a lokacin babban zaben 2023.

Jami’iyyar tace kwamitin zai yi duba ne akan inda jami’iyyar take da rauni da gazawa tare da nemo wasu damammaki hadi da nasarorin da jami’iyyar zata iya samu a zabe mai kamawa.

Jami’iyyar PRP ta ce; “A ganawa ta 62 da Kwamitin zartawar PRP na kasa ya gudanar a ranar 22 ga watan Yuni a garin Kaduna, ya yanke kirkirar kwamitin guda 3 wadanda zasuyi duba tare da yin nazari akan irin rawar da jami’iyyar ta taka a zaben 2019 don fito da hanyoyin da jami’iyyar zata fito da kwarinta a nan gaba.”

Shugaban Jaridar Daily Trust, Malam Kabiru A.Yusuf, Farfesa Momodu Kashim Momodu, Dakta George Kwanashie, Kwamared Ayo Sando, Dakta Obi Osisiogwu da Farfesa Nathaniel Abraham ne suke cikin sauran kwamitocin da jami’iyyar ta kafa.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.