Home SiyasaAisha Kaita: Shekaran jiya tana PDP, jiya ta shiga APC, yau tayi tsalle ta koma PDP

Aisha Kaita: Shekaran jiya tana PDP, jiya ta shiga APC, yau tayi tsalle ta koma PDP

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Wasu daga cikin ‘yan PDP kwankwasiyya da suka sauya sheka zuwa APC Gandujiyya sun sake tsallan bakadai sun dawo gida bayan kwana 1 da sauya shekar tasu.

Majiyar Dabo FM ta tabbatar da dawowar Aisha Kaita wadda aka hango cikin tawagar tsohon shugaban PDP na jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi da mai magana da yawun madugun Kwankwasiyya, Binta Sipikin tayi mi’ara koma baya a daren Alhamis.

Aisha cikin wata hira da madugun kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya gabatar a kafafen yada labarai ta bayyana cewa “Yan Kwankwasiyya kuyi min afuwa, tsautsayi ne ya kaini, hakan bazata kara faruwa ba.”

Da yake karin bayani, Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa ya sahalewa matsan jam’iyyar PDP duk wanda ya samu damar ya wanki yan jam’iyyar APC yaje ya ‘wanki gara’ amma ayi cikin nutsuwa.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00