Ra'ayoyi

Idan har Siyasa ba za ta zama sular ci gaban al’umma ba, bai dace ta rusa su ba, Daga Hassan Ringim

Hassan M. Ringim

Sau da dama a mafi yawa daga cikin harkokin rayuwarmu kama daga addini, siyasa, kasuwanci da fannin tsaro gami da tattalin arziki da kula da lafiya hakanan kimiyya da fasaha(idan akwai), to kai tsaye mu kan yayumo su ne daga kasashen waje sannan mu fara aiwatarwa ko amfani da su a cikin kasarmu, muna masu fatan mu ma mun samu ci gaba da kuma kurarin wuyanmu ya kusa isa yanka.

Daga cikin abin da nake ganin ya zamar mana alakakai wanda muka jajubo daga ketare, akwai siyasa. Wannan siyasa ta kasar Amurka da muka jibgawa kanmu ba tare da nazartar yanda ta Amurkan ta samo asali ba, shi yasa har kawo yau ba wani muhimmin abu da siyasar ta haifar mana idan muka nazarci yanda siyasar ta su ta kafu.

Idan muka dan waiwaya baya kadan, duk zabukan da aka yi a Najeriya baki dayansu kunshe suke da matsaloli gami da kalubale. Kalubalen da har yanzu ba wanda zai ce zai iya warwaruwa. Akwai ma zaben da sai da aka kammalashi cikin lafiya, amma gwamnatin Babangida ta rushe. Wannan zabe na Abiola ba zai taba goguwa a tarihin kasarnan ba.

Akan haka ma ake yi masa lakabi da June 12. Idan har muka fahimci shimfidar da na soma, to ba shakka ashe mun gado matsala ce tsantsa. Matsalar da ta ke ta ci gaba da ruruwa har zuwa yanzu da aka kammala babban zaben kasa a shekarar da ta shude ta 2019.

Wani babban abu da nake ganin ya zamar mana babban tashin hankali a Najeriya shine, yanda lamarin takara da cin zabe gami da faduwa zaben ya kai matakin da za a iya kiransa da annoba. A yau, sanin kowa ne batun hawa layi a kada kuri’a a kirga ace wane yaci ko ya fadi, ya zama tamkar almara. A yau, batun ka hau layi ka kada kuri’a cikin nutsuwa ka koma gida babu tabbas.

A yau, ka futo da bukatar dangwalawa wanda ka ke so, to amma yamutsi ko barazana zai iya cin karfin mutum ya sare, ko ya koma da baya ko kuma wani abu ya sameshi. Duk ba batun matasan da suka sha kwaya, ba a batun jami”yan tsaro marasa amana ba. Ba a ma zancen ma’aikatan zabe da suka kware wajen cin amanar da aka ba su! Idan kuwa har hakane, shin Siyasa a irin wannan yanayi ta dace da mu, kuma ta kawo mana ci gaban da ya dace da yanayin da muke ciki? Wani zai ce ai siyasar da aka karbo, ta bayar da damar samar da romon dimokaradiyya irin su hanya da samar da wuta da ruwa, gami da harkar lafiya da inganta masana’antu.

To naji. Shi kuma garkuwa da mutane, sace-sace, kungiyoyi ta’addanci da su kashe mutane da satar dabbobi gami da uzzurawa talakawa da zalunci, shi ribar mulkin menene? Na turawa ko sarakuna ko kuma mulkin soji? Ya kamata mu mike mu fahimci kamu da kuma sanadin kasancewarmu da juna akan wannan tafarki na siyasa da muke jagorantar kanmu da shi. Sau da dama mun kasa fahimtar wata matsala.

Mafi yawa daga matsalar tsaro ko kalubalen da ake fuskanta a kasa ya kan samo asali ne ta hanyar da ake gudanar da zabe. Misali, mutum ya futo takara amma aka murkusheshi ranar zabe, aka hanashi kuri’un da ya samu. Sannan da yawa daga magoya bayansa sun fahimci hakan.

To daga hakane wasu fusatattu suke fadawa wani yanayi na kalubalantar gwamnati. Wannan yanayi ne idan yayi kamari, sai a yanke kauna da gwamnatin, sai hayaniya sai bore, shikenan kuma sai abin da hali yayi. To don haka yana da kyau hukuma da al’umma su mike su fahimci me adalchi yake nufi kususan a siyasa irin ta Najeriya mai kunshe da sarkakiya da kalubale. Akasin haka kuwa komai na iya faruwa wanda ba zai yi dadin ji da gani ba!

UA-131299779-2