Daga yanzu zamu dinga bayyanawa ‘yan Najeriya kudaden su da muke kashewa a fili -Buhari

Karatun minti 1
Muhammadu Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa daga yanzu babu wani sauran boye-boye tsakanin gwamnatin sa da ‘yan Najeriya saboda zai sa a ringa bayyana kudaden da gwamnati ke kashewa a fili.

Majiyar Dabo FM ta rawaito shugaba Buhari ya fadi hakan ne ta bakin mai taimaka masa a bangaren yada labarai , Garba Shehu, a wani taron yaye dakarun hukumar hana cin hanci da rashawa, EFCC a ranar Talata a jihar Kaduna.

Shugaba Buhari yace ” Zanyi duk mai yiwuwa don ganin babu inda rashawa zata labe a cikin gwamnati na, kokari na shine daga yanzu zamu dunga nunawa duniya kudaden da muke zara daga asusun Najeriya a fili domin kowa ya shaida.”

Furucin dai bai bada mamaki ba duba da yanda gwamnatun ke kokarin yaki da rashawa, sai dai kuma jamiyyun adawa da sauran mutane na ganin yaki da rashawar ana yi ne ga wanda basa goya wa gwamnatin baya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog