Labarai

Muna aiki ta karkashin kasa domin sasanta Sarki Sanusi da Ganduje -Shekarau

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce yana aiki ta karkashin kasa domin ganin an samu masalaha tsakanin gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Majiyar Dabo FM ta jiyo sanatan ne yayin wata ziyara da ya kai ofishin BBC dake birnin Landan, sanatan wanda ke wakiltar Kano ta Tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, ya ce a matsayinsa na daya daga cikin ‘yan majalisar sarki kuma jigo a gwamnatin Kano ba abu ne mai yiwuwa ya fito karara yana tsokaci a kan al’amarin ba.
Domin haka za su ci gaba da aiki ta karkashin kasa don cimma masalaha a tsakanin shugabannin biyu.

Shekarau yana wannan magana ne a karon farko tun bayan fara takun sakar yayin da ya cika shekarara 10 da samun sararutar Sardaunan Kano, wadda marigayi Sarki Ado Bayero ya nada shi.

“Ita masalaha kamar ciwo ce, rana daya sai ciwo ya shige ka amma sai ka shekara, shekaru ma kana shan magani ba ka warke ba,” in ji Shekarau.

Ya kuma bayyana cewa yana sane da kima da martabar masarauta, kana kuma ya san kima da martabar gwamnatin Kano don haka za su ci gaba da yunkurin ganin an sasanta.

Duk da cewa an dan samu sassauci kan bayyanar sabani tsakanin sarki da gwamna, an ci gaba da zaman ‘yan marina tsakaninsu, inda kowa yake harkarsa ba tare da shigar da dayan ba.

A watan Mayun bara ne gwamnatin Kano ta kirkiri sababbin masarautu hudu a Kano, abin da wasu suke ganin an yi ne domin kassara karfi da tasirin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Gwamnati ta ce an kirkiro sababbin masarautun ne domin tabbatar da ci gaba.

Karin Labarai

Masu Alaka

Goggon biri ya hadiye miliyan 7 a gidan namun dajin jihar Kano?

Dabo Online

Dama can nasan Ganduje ne yaci zaben Kano -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Sarki Sunusi ya tsige limami a Kano bayan ya bijirewa umarnin Sarkin Musulmi akan ganin wata

Dabo Online

Zaben2019: Ina kiran magoya bayana da su zabi shugaba Buhari – Salihu Takai

Dabo Online

Masarautar Bichi tayi fatali da umarnin kotu, ta cire rawanin Sarkin Bai da wasu Hakimai 4

Muhammad Isma’il Makama

Kano: CP Wakili ya kama ‘Yan fashi da masu dillancin Kwayoyi 142 a kwana 4

Dabo Online
UA-131299779-2