//
Thursday, April 2

Kofa ya tsugunna mana har kasa don mu roki mutane su zabe shi amma suka ki – Abbas

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban jami’iyyar APC na jihar Kano, Hon Abdullahi Abbas, ya bayyana tsugunawar da tsohon dan majalissar tarayya, Hon Abdulmuminu yayi matsayin roko dan a nema masa kuri’ar jama’a.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin ganawarshi da jaridar KANO FOCUS a ranar Litinin a birnin Kano.

DABO FM ta tattara cewar a ranar Asabar, Hon Aliyu Datti na PDP ta lashe zaben da aka sake na wakilcin kananan hukumomin Bebejji/Kiru a majalissar tarayyar Najeriya da tazarar kuri sama da 20,000.

Haka zalika, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa sunyi duk wani kokari domin ganin Hon Kofa ya koma kan kujerarshi amma abin yaci tura bisa rashin zabarshi da jama’ar yankin sukaki yi.

Masu Alaƙa  Munada Shugaban Ƙasa, 'Yan sanda da Sojoji, ko PDP taci zaɓen Gwamna sai mun ƙwace - Abdullahi Abbas

“Mun yi duk abinda zamu iya da mai girma gwamna, Dr Abdullahi Ganduje, duk da alaka mai tsami tsakaninmu, mun shiga garuruwan Bebeji da Kiru don neman mutane su zabeshi.”

“Hakan ne dalilin da yasa ya samu wasu kuri’un da ya samu a zaben da aka kammala, ina tabbatar maka cewar mutanen yanki basa sonshi shiyasa suka hanashi komawa.”

Ya kuma kara da cewa, Hon Abdulmuminu Jibrin ne ya kayar da kanshi. Tare da tsugunna musu har kasa domin neman su roka masa mutane su zabeshi.

“Shi ya kai kanshi kasa da kanshi. Ya durkusa mana don mu roko mutane su zabe shi.”

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020