Labarai

Ganduje ya tarbi Sarki Sunusi da wakar ‘Sarkin Bichi zai zama Sarkin Kano’ a fadar gwamnati

Amon waka da taken “Gwamna ka kada su Kandala, masu dara ja sun shiga dimuwa, tin da 4-0 ta tabbata, Sarkin Bichi zai shiga Badala” ta cika fadar gwamnatin Kano yayin shigar mai martaba Sarki Muhammad Sunusi II.

A jiya Litinin, sarakunan jihar Kano guda 5 suka kai wa gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ziyarar taya murna bayan nasarar da ya samu a kotun koli kan kalubalantar nasararshi da PDP tayi a zaben gwamna.

DABO FM ta tattara cewa yayin shigar Sarkin Kano, mai martaba, Mallam Muhammadu Sunusi II, zuwa fadar gwamnati, an jiyo tashin sautin wakar da ta kara tabbatar da alakar gwamnatin da Sarkin Kano tana cigaba da yin tsamari.

Haka zalika wakar tayi nuni da yadda rikicin jagoririn biyu yake son kai wa ga sauya wa Sarkin Kano masarauta daga Kano zuwa wani yankin da akafi nuni da Bichi.

Ga yadda karin wakar ya fito, “Gwamna ka kada su Kandala, masu dara ja sun shiga dimuwa, tin da 4-0 ta tabbata, Sarkin Bichi zai shiga Badala.”

DABO FM ta tattara yadda Sardaunan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, sanatan Kano ta tsakiya ya bayyana yadda suke bi wajen shawo kan rashin jituwar jagororin jihar Kano guda biyu.

Sai dai malamin yace yana wannan yunkurin ne ta karkashin kasa tare da cewar a matsayin na mai girmama dukkanin bangarorin, bazai zama mai yin sa baki akan rikicin a bainar jama’a ba, duka dai a yayin tattaunawarshi da sashin Hausa na BBC.

UA-131299779-2