/

Tallafawa al’umma kai tsaye yafi a baiwa gwamnati – Ahmad Musa

Karatun minti 1

Kyaftin na kungiyar kwallon kafan Najeriya ta Super Eagles, Ahmad Musa yayi tsokaci game da yadda masu kudi suke baiwa gwamnati taimako.

Ahmad Musa ya bayyana cewar baiwa gwamnati tallafi domin yaki da cutar Koronabairas bashi da fa’ida.

DABO FM ta tattara cewar dan wasan ya bayyana haka yayin da yake ganawar kai tsaye da sashin Hausa na DW a Instagram a ranar Alhamis.

Da yake amsa tambaya da wakilin DW Hausa yayi masa kan cewar “Masu kudi a Najeriya irinsu Dangote sun bada gudunmawar biliyoyin kudi domin yaki da Koronabairas, ba ka gani mutane suna tsammanin su ji kai ma ka bayar da naka taimakon?

Ahmad ya amsa; “Ahmad Musa ba daya bane da Dangote.”

“Ko da inada biliyan daya ba zan tallafawa gwamnati ba. Gwara in dauki kudin da kai na inje in tallafawa wadanda na san yakamata a tallafa musu amma bazan bai wa gwamnati ba.”

Ahmad Musa ya bayyana irin yadda yayi nashi taimakon a jihar Kano ta hanyar kai tallafi zuwa ga gidajej mabukata.

DABO FM ta tattara cewar Ahmad Musa yana daga cikin ‘yan kwallo a Najeriya da suke taimakon mabukata musamman a lokutan azumi da lokutan da ake tsananin bukatuwar taimakon.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog