Kyaftin din kwallon kafar Najeriya, Ahmad Musa tare da kungiyarshi da Al Nassr ta kasar Saudiyya, sun samu nasarar lashe kofin ‘Super Cup’ bayan doke kungiyar Taawon a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Wasan da aka buga a filin wasa na Sarki Abdullah ranar 5 ga Janairun 2020 ya kai da bugun daga kai sai mai tsaron gida inda kungiyar Al Nassr ta doke takwararta da ci 5 da 4.
Duk da canjin dan wasa Ahmad Musa mintuna 5 kafin bugun fenaritin, Ahmad daya ne daga cikin jigon da suka kai ga kawo kungiyar wasan na karshe a gasar.
Wannan ne kofi na 2 da dan wasan ya samu lashewa tare da kungiyar Al Nassr tin bayan komawarshi kungiyar bayan kammala kofin duniya da akayi a kasar Barazil a shekarar 2018.
Kungiyar Taawon ce ta fara jefa kwallo a ragar Al Nassr a mintuna na 18 da fara wasan ta hannun dan wasanta Leandre Tawamba Kana, dan kasar Kamaru, inda Abderrazak Hamdallah na kungiyar Al Nassr ya farke wa kungiyar mintuna 2 kafin tafiya hutun rabin lokaci.
Al Nassr ta cinye dukka bugun da tayi guda 5 inda Taawon ta zubar da bugu 1.
