//

A tantance jami’an tsaro domin ana zargin akwai hannun su a hare hare -Sheikh Sani Jingir

0

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bukaci a tantance jami’an tsaron kasar nan, don a fitar da batagarin da suke yi wa kasar zagon-kasa a harkokin tsaro.

Majiyar Dabo FM ta rawaito Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana wannan bukata ce a lokacin da yake gatabar da nasiha a Masallacin Juma’a na ’Yan Taya, da ke garin Jos a ranar Juma’ar da ta gabata. Ya ce tantance jami’an tsaron kasar nan, ya zama wajibi ganin irin zargin da ake yi cewa akwai batagari da suke kulla manufanci, a cikin jami’an tsaron kasar nan.

Ya ce, “Muna kira ga kyawawan sojoji da kyawawan ’yan sanda ku tashi tsaye, ku fitar da ’yan Boko Haram da suke cikinku. Domin ana zargin cewa wasu hare-haren ’yan Boko Haram da ake yi a kasar nan, a halin yanzu ba ’yan Boko Haram ba ne munafukai ne. Don haka aka kasa magance wannan matsala.”

Masu Alaƙa  Turawa sunyi amfani da maganganun PDP wajen saka Najeriya ta 1 a cin hanci -Garba Shehu

Sheikh Jingir ya yi kira ga al’ummar kasar nan su tashi su kare garuruwansu daga masu kawo masu hare-hare. Ya ce bai kamata mu rika kwantawa muna barci wadansu ’yan tsirarin mutane su zo su rika tayar mana da garuruwanmu ba.

Sheikh Jingir ya ce “Tsarin karba-karba a kasar nan aikin banza ne, domin ya cutar da Arewa. Don haka ba mu yarda da tsarin karba-karba ba.” Kamar yadda jaridar Aminiya ta DailyTrust ta wallafa.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020