Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Tsaro: Ka daina wasa da hankalin ‘yan Najeriya -Kungiyoyin kare hakkin dan adam ga Buhari

Cibiyar kungiyoyin kare hakkin bil’adama wato ‘Centre for Human Rights and Social Justice’ (CHRSJ) taja kunnen shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da ya daina fadawa ‘yan Najeriya abinda ba haka yake ba akan batun matsalar tsaro data addabi kasar baki daya.

Majiyar Dabo FM ta rawaito jan kunnen na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban cibiyar kungiyoyin, Adeniyi Sulaiman ya fitar biyo bayan kalamin da buhari ya aike ta bakin mai magana da yawun sa, Femi Adesina na cewa yanzu Najeriya babu wata matsalar tsaro kamar shekarar 2015.

Mr Sulaiman yace “Muna sane da shekaru2 baya da ministan yada labaran Buhari, Lai Muhammed ya bayyana an kashe Boko Haram, bayan kuma gashi Boko Haram, Barayin Shanu, Masu Garkuwa da mutane da sauran miyagu sai kara karfi suke a Najeriya.” Kamar yadda DailyNigerian ta fitar.

Masu Alaƙa  Yan soshiyal midiya ne suka dora Atiku a keken bera - Femi Adesina

Daga karshe dai kungiyoyin sun goyi bayan kiran da majalisun kasar nan suka yi na shugaban kasa ya cire shugabannin tsaro, kana da sarawa ga wani kira da shugaban marasa rinjayen majalisar dattijai, Enyinnaya Abaribe yayi na shugaban Najeriyar yayi murabus akan matsalar tsaro.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.