//
Tuesday, April 7

A nuna wa ‘yan Najeriya gawarwakin masu satar mutane 250 da aka kashe -Shehu Sani

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya bukaci hukumar tsaron Najeriya ta nuna kadan daga cikin masu garkuwa da mutane 250 da take ikirarin ta kashe a jihar Kaduna.

Majiyar Dabo FM ta bayyana cewa Shehu Sani yayi wannan furuci ne a shafukan sa na sada zumunta inda ya bayyana “Gani ya kori ji.”

Shehu Sani ya kara da cewa “Shawara ta ga jami’an tsaro shine ya kamata su gayyaci manema labarai domin gani da ido na kawar da fiye da masu satar mutane 250 da suke ikirari, yanzu abubuwa sun koma sai an gani da ido ake yarda.”

Har izuwa yanzu dai sanatan yaki yin gum da bakin sa duk da binciken da hukumar EFCC take masa, wanda makon da ya wuce ya samu beli bayan ta tsare shi kusan wata guda, bayan fitowar sa ya bayyana cewa a dakin tsare mutane na karkashin kasa a ka saka shi.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020