//

Mu da muke da madafun iko bamaso a fada mana gaskiya – Zulum

0

Babagana Zulum, gwamnan Borno ya bayyana cewa yanzu fadan gaskiya ya zama matsala a Najeriya, ya fadi haka ne a wani taro da manyan shugabannin tsaro na gida Najeriya dama kasashen waje a Abuja.

Majiyar Dabo FM ta bayyana cewa gwamnan na Borno yayi wannan furici ne a ranar Talata a kwalejin tsaro ta kasa, babban birnin tarayya dake Abuja, kamar yadda TheCable ta fitar.

Zulum yace “Shugaba mai dabara shine shugaban da yake da kwazon sauraro da karanta duk abinda yake faruwa, shugaba mai dabaru na tinani shine mai dabarun koyon abinda bai sani ba, shugaba mai kwazo shine mai bude kunnuwan sa domin a fada masa gaskiya kana yayi aiki da ita.”

Masu Alaƙa  Boko Haram: A jihar Borno kadai, mutane sama da dubu 140 ne suka yi gudun Hijira a shekarar 2019

“Mutane da dama baza su taba gaya maka gaskiya ba idan kana kan mulki, haka muma da muke kan mulkin bama so ko kadan a gaya mana gaskiya.” Wannan kalamai sun zo ne cikin wata takarda wadda gwamnan ya amsa gayyatar kwalejin mai taken “Dabarun Shugabancin: Kalubale a kan tsaron jihar Barno.”

Duk baki daya wannan yazo bayan wani gamo da gwamna Zulum yayi da sojoji a kan hanyar Damaturu zuwa Borno cikin watan Junairu wanda ya daga wa sojojin murya kan abinda ya kira da suna cutar da masu amfani da titin wajen karbar na goro.

Daga bisani dai hukumar sojin Najeriya ta bayyana abinda gwamnan yayi wa sojin dake kan aiki zai iya shafar yakin da suke da Boko Haram.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020