Babban Labari Labarai

MSSN ta raba kayan abincin ga mabukata a Zariya

A kokarin ta na inganta rayuwar al’umma da tallafa masu da kayan abinci a wannan wata mai Alfarma, Kungiyar ‘Yan uwa musulmi ta kasa shiyyar A. da ta kumshi jihohi 19 na Arewacin Najeriya ciki har da Abuja, wato “Muslim Student Society of Nigeria, Zone A”. ta raba kayan abinci ga mabuka da marasa galihu har ma da marayu.

Rabon kayan abinci da ya gudana a sakatariyar Kungiyar da ke Zangon Shanu Samarun Zariya, a Jihar Kaduna. akalla mabuka 20 suka amfana daga rabon.

Da yake ma Dabo FM cikakken bayani akan hanyoyin da suka bi wurin bada tallafin, Shugaban kwamitin shirin Dakta Adamu Aliyu, ya ce, wannan shi ne kashi na farko na rabon kayayyakin tallafin, shi ya sa aka zabi mutane kalilan domin su samu hatsi mai yawa da zai amfane su na tsawon lokaci. Ya ce, kokarin na su ba wai ya tsaya ne kadai ga rabon kayayyakin abinci ba, su kan raba tsabar kudi musamman ga mabukata da ma wayar da kan Jama’a musamman game da cutar sarkewar numfashi ta Covid-19 da ke damun al’umma a yau.

Ya kara da cewa, shirin rabon kayan abincin, an saba gudanar da shi duk shekara, sai dai na bana ya zo ne dai-dai lokacin da al’umma ke zaune a gida saboda dokar kulle da gwamnati ta sanyawa saboda kokarin dakile yaduwar cutar Covid-19.

Dakta Adamu Aliyu, ya hori sauran kungiyoyi da dai-daikun al’umma su dukufa wurin taimakawa gajiyayyu da marasa karfi a irin wannan lokacin.

A jawaban su daban-daban, wasu daga cikin wanda suka amfana da tallafin, Malam Aliyu Umar da Malam Sani Ibrahim da kuma Malam Yunusa Abdullahi, sun nuna matukar farin cikin su ne tare da godiya ga Kungiyar ta MSSN bisa tallafin da ta ba su, kuma su ka yi fatan Allah Ubangiji ya saka da mafificin Alheri.

Karin Labarai

UA-131299779-2