Fitacciyar jarumar, Rahama Sadau ta kammala karatun ta jami’ar Eastern Mediterranean University dake birnin Famagusta a kasar Cyprus. Ta kammala karatun ne a fannin “Human Resources Management”. Jarumar ta shiga sahun jarumawan na Kannywood masu shedar kammala karatun jami’a.