0
Idris Abdulaziz Sani
- Kyautatawa sadaka da ciyarwa a cikin hanyar Allah: Allah ya fada a cikin Alqur’ani, “Wadanda suke ciyar da dukiyoyinsu dare da rana, masu yi a boye ko a fili domin Allah sakamakonsu gidan aljanna.
- Kyautar da Al-Kur’ani ga wani. Duk lokacin da mutum ya karanta daga gare shi zaka samu lada.
- Bada sadakar keken daukar marasa lafiya a asibiti.
- Gina masallaci ko bada tallafi wajen ginawa.
- Gina rijiya ko ajiye randar ruwa duk sanda wani yasha Allah zai baka lada
- Shuka bishiya duk sanda wani yasha inuwar ko yaci irin bishiyar zaka samu lada.
- 7.Neman mutane zuwa ga ayyuka na kwarai: Annabin tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, “Duk wanda ya jagoranci mutum zuwa abu mai kyau, to yana da sakamako iri daya kamar wanda ya aikata aikin”.
- Biyayya ga iyaye mutum: Wannan ita ce babbar hanyar samun yardar Allah da aljanna.
- Fadin gaskiya duk wahalar ta.
Shawarar DABO FM
Dukkanin aiki baya yiwuwa sai da niyya. Ma’ana ko mutum ya aikata abinda mai rubutu ya rubuta, a sama, idan babu kyakkyawar niyya to zai tashi a iska.
Malamai sunyi bayanin Niyyar da Hadisin niyya yazo dashi cewar; Niyya ba tana nufi kudurcewar yin aiki bane. Tana nufin MANUFA.
“Dukkanin ayyuka basa yiwuwa sai da manufar yi dan Allah.”
