Batan Mutane: Ya fita daga gida zuwa wajen aiki, tsawon kwanaki 3 ba’a ganshi ba

Hamza Dalhat Fagge, Malamin makarantar Firamare a karamar hukumar Fagge, ya bata bai dawo gida ba.

Iyalan Malamin, sun sanar da Dabo FM cewa, “Ranar Lahadi ya fito daga gidanshi dake unguwar Ja’in a inda ya nufi unguwar Fagge, mahaifarshi, inda kuma yake sana’ar dinki da misalin karfe 2 na rana.”

Sun bayyana cewa tin daga ficewarshi a ranar Lahadi, har zuwa yau Talata, bai samu dawowa ba.

“Tin daga nan bamu sake ji daga gareshi ba, mun buga waya Fagge, sunce bai je ba, muma bai dawo mana ba.”

Rahotanni daga rundunar ‘yan sandan jihar Kano, sun bayyana basu samu labarin tsintar bawan Allah ba, sai dai sun tabbatarwa da iyalanshi cewa; “Da zarar sun samu inda yake, zasu tuntubesu.

Masu Alaƙa  Yadda za mu kare kan mu daga kamuwa da cutar zazzabin 'Lassa' -Dr Abdul'aziz T. Bako

Mallam Hamza Dalhat Fagge, siriri ne fari, mai kuzari, bashida matsalar lafiya ko ta kwakwalwa.

Ya bata ne a cikin koshin lafiya.

Ana kira ga al’umma cewar duk wanda ya samu ganinshi, yayi kokari ya mika shi ga hukumar ‘yan sanda a ofishinsu mafi kusa dashi.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.