Labarai

Karin girma yafi karin N600 a albashi – Malaman Firamare a Kano sun koka

An wallafa ranar 3/01/2020, anyi gyara 07/01/2020

Malaman dake koyarwar a Firamare na jihar Kano sun bayyana kokensu bisa fara biyan sabon albashi da gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Ganduje tayi.

Malaman sun koka kan yacce suka ce basu samu karin albashin ba duk da sune yakamata ace an karawa kudaden domin irin gudunmawar da suke bawa yara masu tasowa.

DABO FM ta zanta da wasu daga cikin malaman jihar da kuma wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu a dandalin na sada zumunta.

Wasu daga cikin Malaman sun bayyana mana cewa karin 600 kacal suka samu a sabon albashin da gwamnatin ta fara biya a daren 1 ga watan sabuwar shekarar 2020.

“N600, kacal aka karamin akan abinda ake bani, mafi yawan lokaci ma ba’a bamu albashin akan lokaci.”

Ya bayyana cewa kusan kowanne lokaci ana fara yi wa manyan ma’aikata dake aiki a matakin jiha kafin su a waiwaye su.

Shi ma wani malamin Firamare da muka zanta dashi, yace; “An bar farilla an bige da nafila, ayi karin girma yafi a kara albashin.”

Bayan kwarya kwayar bincike, DABO FM ta tattara cewa malan Firamaren Kano basu samu karin albashin da yafi N2000 ba, yayin da wasu ma’aikatan a wasu ma’aikatu a jihar dake da matakin aiki iri daya da malaman, sun samu karin N6000,

Kusan kowane lokaci, a Najeriya, Malaman Firamare suna fuskantar kuntatawa daga bangarorin gwamnati domin wani sa’ilin Malaman suke siyan kayan karatu irinsu alli, domin koyar da daliban.

Mafi akasari idan ba masu uwa a bakin murhu ba, sukan shafe shekaru masu tarin yawa kafin ayi musu karin girma na aiki.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kishi: Wata mata ta rikito da mijinta daga bene, bayan da tace ya cije ta

Dabo Online

Gidauniyar Kwankwasiyya ta kai karin dalibai kasar Dubai da Sudan domin karatun digiri na 2

Muhammad Isma’il Makama

Sarki Sunusi ya tsige limami a Kano bayan ya bijirewa umarnin Sarkin Musulmi akan ganin wata

Dabo Online

Ganduje, Sarki Sunusi sun jagorancin daurin auren Zaurawa 70

Dabo Online

Kano: CP Wakili ya kama ‘Yan fashi da masu dillancin Kwayoyi 142 a kwana 4

Dabo Online

Likitoci sunyi tiyatar kwakwalwa ta farko a jihar Kano

Dabo Online
UA-131299779-2