//
Thursday, April 2

Yanzu Yanzu: DSS ta cafke mutumin da ya fito da labarin auren Buhari

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Jami’an tsaro na farin kaya sun kama mutimin da yayi kirkira da watsa labarin karya na auren Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da Ministar sa Sadiya Faruoq.

Kakakin DSS, Peter Afunaya ne ya sanar da haka yayin taron manema labarai a ofishin hukumar dake garin Abuja.

DABO FM ta tattaro Afunaya ya bayyana cewa hukumar ta kama mutumin ne bisa korafi da Sadiya Umar Faruk din ta shigar a gaban hukumar.

Kakakin ya kuma yi kira da ‘yan Najeriya da su kiyaye yada labaran karya a kafofin sadarwa domin samun zaman lafiya a kasa baki daya.

Cikakken labarin na nan tafe..

Masu Alaƙa  Halayyar Buhari ta gaskiya ta bayyana bayan darewarshi shugabancin Najeriya - Buba Galadima

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020