RAJASTHAN: Sanarwa da gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya fitar ta hannun kwamishinan yada labarai, Muhammadu Garba ya fitar, yace har yanzu akwai dokar zaman gida a jihar Kano.
DABO FM ta tattara cewar gwamnatin tarayya ta sassauta dukkanin dokar zaman gida a fadin Najeriya tare da bai wa gwamnoni damar bada izinin bude Masallatai da Coci dake fadin Najeriya.
“Dokar hana zirga-zirga ta koma daga karfe 10 na dare zuwa 4 na asuba.”
A cikin sanarwa da gwamnatin Kano ta fitar, Gwamna Ganduje ya amince da bude dukkanin kasuwanni dake fadin jihar Kano. Sai dai fa gwamnan ya ce za a bude kasuwannin ne a iya ranakun da gwamnatin jihar ta amince a bude gari.
DABO FM ta tattara cewar ranakun da gamnatin Kano ta ware sun hada da Laraba, Juma’a da ranar Lahadi.
