/

Ku bi umarnin gwamnati tare da girmama shawarwarin masana kiwon lafiya – Sarkin Zazzau

Karatun minti 1
Sarkin Zazzau
Mai martaba Alhaji Shehu Idris -Sarkin Zazzau

Sarkin Zazzau, mai martaba Alhaji Shehu Idris, ya yi kira ga al’umma da su bi umarnin gwamnti tare da bin duk shawarwarin masana kiwon lafiya domin dakile yaduwar cutar Kwabid19.

Sarkin ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya gabatar wa manema labarai yau Laraba a fadarsa da ke birnin Zaria na jihar Kaduna.

Ya sanar da Jama’a cewa cutar na nan bata kau ba, kuma tana cigaba da yaduwa tsakanin al’umma, don haka jama’a sai sun taimaki kansu da kansu domin hana cigaba da yaduwarta.

Sarkin ya kuma ya umarci daukacin hakimai, dakatai da masu unguwanni da kuma ardo-ardo da ke kafatanin jihar Kaduna da su dauki matakan wayar da kan al’ummar ta kowacce fuska domin fahimtar da su abubuwan da suka kamata.

Taron da DABO FM ta halarta, mai martaba Alhaji Shehu Idris, ya nanata muhimmancin cigaba da wanke hannu da sabulu da sanya takumkumin rufe fuska da kuma takaita shiga cunkoson jama’a domin a cewarsa ta haka ne za a samu saukin yaduwar cutar.

Daga nan sai mai martaba Sarki, Alhaji Shehu Idris, ya bukaci ganin ana sanar da jami’an kiwon lafiya cikin gaggawa da zarar an samu wani da alamun cutar suka bayyana a jikinshi.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog