An kama wani jami’in Karota babu wando lokacin da yake gab da fara yi wa yarinya lalata a Kano.
Jami’in da aka bayyana da sunan Umar Yakubu Muhammad, yana daga cikin jami’an da suke aiki domin tabbatar da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya a yunkurin da takeyi na yakar cutar Kwabid-19.
Jami’in rundunar ‘yan sanda dake aiki a katafaren kantin Ado Bayero Mall ne ya kama dan Karota babu wando a jikinshi, kamar yadda Daily Trust ta bayyana.
Jami’in Karotan ya karyata zargin inda ya yi ikirarin ya dauko ta ne domin ya taimaka mata ya kai ta gida. Gidan da a cewarshi yake bayan kasuwar Baje Koli ta ‘Trade Fair’ a jihar Kano.
Sai dai yarinyar ta bayyana cewar ta san jami’in Karotar, sanin da mata take yi wa mijinta.
Zuwa yanzu haka dai dukkaninsu su biyu suna ajiye a ofishin ‘yan sanda dake Kwalli.