Labarai

Ya kamata gwamnati ta kara kaimi wurin wadata ‘yan kasa da kayayyakin more rayuwa-Abba Adamu

A dai-dai lokacin da ake kukan tsadar rayuwa saboda sanya dokar takaita zirga-zirgan a wasu jahohin kasar nan da gwamnatin tarayya ta yi, an bukaci ‘yan kasuwa musamman masu sayar da hatsi su yiwa Allah kada su kara farashin kayayyakin masarufi saboda yanayin da aka shiga a kasar nan.

Wani jigo a Jama’iyyar Apc a karamar hukumar Taura da ke Jihar Jigawa Hon Abba Adamu Aliyu ya bayyana hakan sa’ilin zantawar sa da Dabo FM.

Ya kwatanta halin da ake cikin a matsayin wani jarabi daga Allah madaukakin Sarki, ya kuma nuna bakin cikin sa kan yadda wasu ke amfani da wannan lokaci wurin tsawwalawa mabukata da marasa karfi duk da halin kunci da al’umma ke ciki.

Ya kara da cewa, ba yanzu ne karo na farko da ake samun annoba ba, ko zamanin annabawan Allah da sahabbai an samu jarabi ta annoba. Sannan ya yi fatan samo maganin ta nan bada jimawa ba.

Da ya juya ga bangaren gwamnati kuwa, Hon Abba Adamu Aliyu, ya naimi ganin ta wadata al’ummar ta da kayayyakin more rayuwa da zai inganta jin dadin su, sannan ya yaba ma shirin gwamnati na ciyar da mabukata a irin wannan lokaci.

Ya yabawa manufofin gwamnatin Jihar Jigawa karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Badaru Saboda yanda al’umma za su dara musamman a irin wannan lokaci.

Karin Labarai

UA-131299779-2