Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje
Labarai

Ganduje ya sassauta dokar hana fita a Kano

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sassauta dokar  hana fita a jihar Kano domin bai wa mutane damar yin siyayyar azumi.

DABO FM ta tattara cewar a ranar 27 ga watan Afrilu, jihar Kano ta shiga dokar hana fita  da shugaba Buhari ya sanya ta tsawon mako 2.

Yayin sanar da matakin sassauta dokar ta hana fita, Ganduje ya bayyana ranakun  litinin da  alhamis, a matsayin ranakun da al’umma domin siyya.

Haka zalika ya bayyana cewar kasuwannin ‘Yankaba da ta Rijiyar Lemo ne kawai gwamnati ta sahalewa budewa da manyan shaguna da suke siyar da kayyakin amfanin yau da kullin.

Sai dai yace za a rika fita ne daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma.

 

 

Masu Alaka

Yanzu-yanzu: Ganduje ya sanya dokar hana fita a Kano, masu Covid-19 a jihar sun zama 4

Dabo Online

Bude gidajen kallon kwallon kafa da Ganduje ya yi a Kano ya bar baya da ƙura

Dabo Online

Kwabid19: Zamu gwada daukacin Almajiran Kano – Ganduje

Dabo Online

Yanzu-yanzu: Mutum 2 sun kamu da Koronabairas yau a jihar Kano, jumillar 313

Dabo Online

An zargi wanda ya kamu da Kwabid-19 a Kano da shigar da cutar da ‘ganganci’

Dangalan Muhammad Aliyu

Ganduje ya bayar da umarnin dinka takunkumin kariya miliyan 1

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2