Home NajeriyaMatsalar Tsaro: ‘Buhari ya gaza’

Matsalar Tsaro: ‘Buhari ya gaza’

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments
Shugaba Buhari ya gaza

Jaipur, India (DABO FM) – Biyo bayan munanan hare-haren da mayakan Boko Haram da ‘yan Binduga dadi suka kai a yankunan arewacin Najeriya da yayi janyo asarar rayuka sama da 150 a cikin ‘yan kwanakin nan, mutane da yawa sun taru kan cewar shugaba ‘Buhari ya gaza’.

Rahotanni sun tabbatar da yadda mayakan Boko Haram suka kashe mutane 81 a garin Borno ya yinda ‘yan Binduga da di suka hallaka sama da mutane 18 a jihar Katsina.

DABO FM ta yi duba kan yadda ‘yan Najeriya a kafafen sada zumunta suka bayyana rashin gamsuwarsu da yadda shugaba Buhari ya ke tafiyar da sha’anin tsaron Najeriya.

A bangaren masana da masu fashin baki, su na ganin ko kadan mutane ba su yi laifi kiran gwamnatin Buhari wacce ta gaza a sha’anin tsaro ba duba da cewar matsalar tsaron ce ta kawo gwamnatin a shekarar 2015.

Babban abin dubawa shi ne zargin da ake yi wa shugaba Buhari na nuna halin rashin ko in kula da yadda ake kashe al’ummar Arewacin Najeriya.

“Ba ya aike sakon jaje balle ya je da kanshi” – cewar wani matashi a kafar Facebook.

Wasu daga cikin hare-haren kwanakin nan:

  • A ranar 20 ga Afrilun 2020, rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina ta tabbatar mutuwar mutum 47 sakamakon harin ‘yan Binduga a rana daya.
  • Kazalika rahotanni sun tabbatar da mutuwar mutum a kalla 40 a wani harin ‘yan bindugar suka kai karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a jiya Laraba 10 ga Yuni 2020.
  • Cikin kasa da makonni biyu, ‘yan Bindugar dai suka kashe dagacin garin ‘Yan tumaki dake garin karamar hukumar Dan Musa.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00