Home LabaraiBabban LabariKungiyoyin Izala da Darika sun gudanar da taro a Kaduna

Kungiyoyin Izala da Darika sun gudanar da taro a Kaduna

by Mu’azu A. Albarkawa
0 comments

Gamayyar hadin kan kungiyoyin addinin Islama ta Jihar Kaduna da suka kumshi bangaren Izala da Darika da suka kira kansu da United Muslim Foundation, wanda Shugaban Kungiyar Fityanul Islam ta Jihar Kaduna Sheikh Rabi’u Abdullahi ke jagoranta da Sheikh Tukur Isah Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa’ikamatusSunnah ta Jihar Kaduna ke matsayin mataimaki, sun gudanar da taro domin wayar da kan mabiyan su game da halin da ake ciki da muhinmancin hadin kai a irin wannan lokaci da duniyar musulunci ke fuskantar kalubale ta ko’ina.

Taron da ya gudana a Zariya ta Jihar Kaduna, ya samu harlartan Malamai da dama da suke wa’azi karkashin Kungiyar Izala da bangaren Darika hadi da shuwagabannin dukkanin bangarorin.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Shugaban Kungiyar ta Jaha Sheikh Rabi’u Abdullahi ya ce, haduwar su koda yaushe suna yin sa ne da nufin kara tattauna damuwar musulmin Jihar Kaduna, domin kara dunke barakan da ke tsakanin su tunda duka an yarda babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, kuma duka an yarda Shika-shikan musulunci biyar ne kana an Ka’aba ake fuskanta duk lokacin gudanar da salloli.
Tunda abun da ya hada daukacin al’ummar musulmi ya fi abun da ya raba su, Ashe ya zama wajibi samun irin wannan hadin kan domin tafiya da murya daya.

A cewar sa, sun yi amannar haduwan da suka yi, sun yi shi ne domin cika umarnin Allah madaukakin Sarki da ya umarci a hadu karkashin tutar sa babu rarrabewa tsakani.

Ya kuma nuna godiyar sa ga gwamnatin Jihar Kaduna bisa sassauta dokar hana zirga-zirga da ta sanya tare da bada umarnin cigaba da Sallar Juma’a cikin Jam’i, bayan da aka kwashe fiye da Sati Goma Sha Daya ba’a yi ba a Jihar Kaduna saboda dokar da aka sanya.

Sai dai ya sake mika koke da kuma roko ga gwamnan, ya sake bude kasuwanni saboda su ma su cigaba da gudanar da harkokin su na yau da kullum kamar yadda aka saba.

Rabi’u Abdullahi, ya kuma naimi masallatan Juma’a su yi duk mai yiwuwa wurin cika ka’idojin da gwamnatin Jihar ta shimfida domin bude masallatan. Kamar sanya naburar gwajin zafin jiki da sabulun wanke hannu da kuma sanya masallata amfani da kyallen rufe fuska.

Da yake nashi jawabin Mataimakin Shugaban Kungiyar kuma shugaban kungiyar Izala ta Jihar Kaduna Sheikh Tukur Isah, ya ce a halin da ake ciki babu wata al’umma da za ta cigaba ba tare da hadin kai ba, shiyasa ma suka kira irin wannan taron a irin wannan lokaci domin fahimtar juna da kuma samun murya daya da za’a rika magana karkashin ta.

Sannan kuma taron nasu ya sake mayar da hankali kan sassauta dokar kulle da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi a makon nan da muke ciki, sai dai ya nanata ganin gwamnati na sanya malaman addini a tsarin ta koda yaushe domin bayar da shawar-wari da nufin samun magani game da cutar da take damun al’umma.
“Kasancewar babu wata cuta da aka saukar sai da Allah ya saukar da maganin ta, kuma addinin musulunci ya koyar da yanda za’a naimo tare da sarrafa irin wadannan magungunan, don haka akwai bukatar gwamnati ta rika gayyatar malamai masana magunguna ba wai na kimiyya kadai ba domin samun maslaha”, a cewar Tukur Isah.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00