Ya kamata Buhari ya rika yi mana jaje ko ta’aziyyar mutuwa – ‘Yan Kannywood da Shugaba Buhari

dakikun karantawa

Jaruman Kannywood sun ce lokacin ya yi da ya kamata shugaba Buhari ya rika yi musu jake ko ta’aziyya idan dayansu ya mutu.

Jarumar masana’antar, Mansura Isa ce ta fara yin ƙorafin bayan shugaba Buhari ya miƙa sakon ta’aziyyarsa ga mawaki Abdulganiyyu da aka fi sani da Sound Sultan ta hannun Femi Adesina.

Mansura ta ce; Baba Buhari, tin da a ke mana Mutuwa a Kannywood ba ku taɓa mana jaje ba, ko gaisuwa na rashi ba. Amma duk sanda yan Kudu wani abu ya samesu ku ne na farkon jaje.

In baku jawo naku a jiki ba, wa za ku ja jiki ? Masu girma Dr Zainab Shinkafi da Mamanmu Aisha Buhari ne kadai su ke bamu goyon baya kuma muna yaba musu.

Amma za mu ji dadi in ka nuna mana ƙauna muma Baba Buhari.”

Ta cigaba da cewa; Mu ne ku fa, duk Alheri da muka samu AREWA muke kawowa domin a amfana. Dan Allah a duba wannan Abu Baba.

Daga ƙarshe dai Mansurar ta ce ta karkata akalar sakon zuwa Bashir Ahmad, daya daga cikin masu taimaka wa Shugaba Buhari a fannin yada labarai.

“Bashir Ahmad, kai ne ya kamata ka yi wannan, domin shima Adesina yana gyara nasu mutanen. Kuma ina da yakini cewa kasan irin gwagwarmaya da muke wa gwamnatin nan, duk da zagin mu da a ke yi a kanku. Dan haka muna jiran sakon ta’aziyyarmu ga wadanda muka rasa musamman ta mamanmu Haj Zainab Booth.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog