/

Ba ni da shirin koma wa APC – Kwankwaso

Karatun minti 1
Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya nesa kanshi daga raɗe-raɗin da a ke yi cewar zai sauya sheƙa daga PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.

Kwankwaso ta hannun hadimin a kafofin yaɗa labarai, Saifullahi Muhammad, ya ce batun sauya sheƙar Kwankwaso ba gaskiya bane.

Ya bayyana haka ne cikin wata tattaunarsa da sashin siyasa na Jaridar Daily Trust.

Kazalika Kwankwaso ya ce bashi da shirin koma wa APC ko kuma wata jami’iyyar domin a yaƙi PDP a zaɓen 2023.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog