Home FadakarwaNasihar Mako: Alƙiblar Iyalanki tare da Aisha Usman Liman

Nasihar Mako: Alƙiblar Iyalanki tare da Aisha Usman Liman

by Dabo Online
0 comments

Assalamu alaikum

Idan muka dauki kalmar alkibla muka bude ma’anarta, a taikaice za mu iya cewa kalmar na nufin fuskantar wani bangare da zai iya zama bagire na madogarar wani abu, ko na matsayar wani abu, ko hadin kan wani abu, ko kuma abun dubi da yin kwaikwayo ko kuma neman fahimta ko maslahar wani abu, ya dai danganta da abunda aka nemi alkibla ko aka maida shi alkibla don bukata.

Mu dauki misali da Ka’aba a matsayin alkibla ga musulmi, ta kasance alkibla ne, don nufin fuskantar Allah ga bauta, amma ba ita ce abin bautar ba. Manzon Allah ya ce, ” duk da Allah na nan a ko’ina, kuma yafi kusanci da mu fiye da jijiyar gefen wuyanmu, wadda rai ke kai komo a cikinta, amma kuma ya yassare muna alkibla abin fuskanta yayin nufin Allah da bauta”. Hikimar hakan kuwa na nuni da samawa bayi nutsuwa da kimsa musu tamkar fuskantar Allah ne, yayin fuskanta alkibla da nufinsa da bauta.

Idan da ace babu ta’ada ta fuskantar alkibla a yayin nufin Allah a cikin bauta, da wata kila an samu ruɗani ko wasiwasi ga wasu zukata a cikin yakinin samuwar Allah ko bauta masa. Da ba a dauki wani abu a matsayin alkibla ya yi zartar da wabi abu ko faruwar wani abu ba, da wata kila ba a samu maslahar yuwar samunsa ko daidaituwarsa ba. Da ana yin magana ko ana jin magana ba tare da dorata kan fuskantar alkiblar da ta dace da ita ba, da ba ta yanda za a iya fahimta ma’anarta, anfanita ko illarta.

Wadan nan duk misalai ne don mu kara fahimtar kalmar alkibla, ta yanda idan aka dorata kan Uwa mace zamu kara fahimtar ko baiwa uwa mukamin caccantar ta zama alkibla ga iyalanta ko akasin hakan.

Idan Allah ya kaimu wani sati lafiya, zamu dora daga inda muka tsaya in sha Allahu.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00