Mawakin Peter Okoye na tsohon kamfanin Square Records da aka fi sani da PSquare, ya yi Allah-wadai da kisan da a ka yi wa Hausa a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Ya bayyana haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.
A karshen makon nan ne dai wasu ‘yan ta’adda mazauna jihar Oyo su ka afka wa Hausawa mazauna garin tare da tilasta musu barin gidajensu.
DABO FM ta tattara cewar a ƙalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu a harin ta’addancin.
Mawaƙin ya ce kisan kiyashin sam bai dace kuma abin ƙi ne mai barazana ga zaman lafiyar Najeriya.
“Ni Inyanuri ne wanda ya auri Bayerabiya. Na girma a Arewancin Najeriya, a can na yi makaranta kuma na fara harkokin waƙe-waƙe na a can. Yanzu haka ina jin Hausa sosai.”
Wai me yake faruwa ne? Ya kamata mu dena nuna wariyar nan da kabilanci. “A dai na zubar da jinin nan.”
