Ra'ayoyi

An bukaci dan Majalissar Tarayya na Fagge ya dena bautar da Matasa da sunan nema musu aikin yi

Tabbas babu inkari dangane da ikirarin da wasu mutane suke yi na cewa dan majalisar tarraya mai wakiltar karamar hukumar Fagge, yana kokari gurin samawa matasa gurbin aiki, kuma har yanzu al’ummar wannan karamar hukuma bata taba samun dan majalisar da yayi makamancin wannan yunkurin ba a baya.

Kuma akwai bukatar ya kara dage dantse gurin nemawa al’ummar da yake wakilta dukkan abubuwan da zai kawo musu cigaba ta fuskoki daban-daban.

Koda yake har yanzu mutane na kalubalantar wanarabul da daukar wasu guraben aiki na wannan karamar hukuma (Fagge) ya kai wasu kananan hukumomin wanda suma suna da nasu dan majalisar, wanda yin hakan zalinci ne mudulakan kuma ya sabawa dukkan wani tunanin mai tunani.

A bangare guda kuma alamu na zahiri sun bayyana, wanda suke nuni da cewa duk kokarin da wanarabul yake yi gurin nemowa wadannan matasan gurbin aiki ana yi ne ta hanyar bautar da masu neman wannan aiki, a inda zaka ga mutum ya zama dan banbadanci da tumasancin dole kawai don a yarda cewa kana tare da shi sannan a baka gurbin aikin yi.

A maimakon ace ana gudanar da wani gwaji (Jarrabawa) da zai nuna kwazon mutum sannan a duba inda yafi cancanta dashi a bashi, kawai sai dai kaga ana shelanta wadannan masu tumasancin a kafar sada zumunta cewa sun samu gurbin aiki.

Abin mamaki a nan shi ne, koda ace ka kasance kana goyon bayan dan majalisar tarrayar, idan ba daga wani bangare kake ba ko kuma ba wani mutum ne ya kawo sunan ka ba to zaman kare a karofi kake yi.

Uwa uba ballantana wanda basa goyon bayan wanarabul kar ma suyi tunanin samun wannan damar duk kokarin mutum kuwa!

Ya kamata shi wannan dan majalisar ya sani cewa bafa iyaka wadanda suke masa banbadanci a kafar sada zumunta kawai yake wakilta ba kuma kowane dan jam’iyya yana da hakki a wuyan sa wanda idan bai yi kokarin saukewa a nan ba dole zai sauke a daya duniyar.

Mun san cewa babu wata sadarar a kundin tsarin mulkin Najeriya da tace sai al’umma sun yi tumasanci ko roko gurin wakilin su sannan zai aiwatar da abin da ya wajaba a gareshi, kuma ina so wadannan matasa masu aikata tumasanci a wannan kafar da zummar samun gurbin aiki su sani cewa tun kafin wanarabul ya samu dama wasu mutanen suke bawa matasa gurbin aiki kuma ba ance daga kan dan majalisar tarraya an daina bada gurbin aiki ba kenan.

Sai ya gushe sannan wani zai fara nashi, kuma tun kafin wanarabul ya fara shi yake yin nasa taimakon kuma ba ayi masa tumasanci a wannan kafar sada zumuntar.

Ya maigirma dan majalisar tarraya, ya kamata ka kara yin duba na tsanaki akan matsayin al’ummar da kake wakilta da kuma yaran ka a siyasance da kake kira ‘Main Kwamiti’, idan har wadancan gungun makarraban naka zasu karbi kowane umarnin tare da yi maka biyyaya akan duk abin da zuciyarka take so to ban tunanin mu al’ummar da kake wakilta zamu yadda da wannan salon bautar.

Idan har mu da muka bada damar a wakilce mu ba za ayi mana abin da ya dace damu ba, to babu yadda za’ayi mu kyale wannan cin kashin yayi ta tafiya, wadancan makarraban naka basu da wani zabi face su bi umarninka koda ko ace ya sabawa al’ummar da kake wakilta domin su bukatar su gaba take da ta kowa.

A takaice dai muna so muga an kawo karshen bautar da matasan wannan karamar hukuma da akeyi da sunan nema musu gurbin aiki, ai ba dole sai mutum ya rubuta “Goro alheri ne” za’a samar masa aiki ba duk da cewa aikin da ya kamata ace anayi a majalisar bashi ake yi ba wanda hakan yasa ake ganin samar da gurbin aiki a matsayin kokari. 

Zan kara hankado guraren da wanarabul ya gaza ko ya gyara, don naga kamar  su tsoron fada masa gaskiya suke saboda abin da suke kaiwa bakin su dana iyalansu.

Rattabawa

 Umaru Aliyu Musa. 

[email protected]

Karin Labarai

UA-131299779-2