//

Bauchi: Mutane 38 ne suka nutse bayan kifewar wani jirgin ruwa

0

A ‘kalla mutane 38 ne suka bace bayan jirgin kwale-kwale ya kife da mutane 40 a Kirfin jihar Bauchi.

Rohotannin da suke fitowa daga karamar hukumar Kirfi, dake jihar Bauchi sun nuna cewa mutum 2 kawai aka iya samun gawarwakin su zuwa yanzu.

Dabo FM ta samu rahoton daga jaridar Independent, inda shugaban ruko na karamar hukumar Kirfi, Alhaji Baffa Abdu Bara, Dan Malikin Bara ya shaidawa manema labarai yanda wannan iftila’i ya auku.

Dan Malikin Bara yace “a ranar litinin 7 ga oktoba da safe jirgin kwale kwale ya dauki mutane 40 inda iftila’i ya auku jirgin ya kifi da mutanen baki daya, yanzu haka mun samu gawar mutum 2 sauran 38 kuma har zuwa yanzu babu labarin su”

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020